Labarai
Ban koma gida na ɓuya ba- Muhammadu Bazoum
Al’ummar Jamhuriyyar Nijar na ci gaba da bayyana ra’ayoyin su game da raɗe-raɗen da ake yi na cewa shugaban ƙasar Bazoum ya ƙauracewa kwana a fadar gwamnatinsa, saboda tsoron juyin mulki dake faruwa a wasu ƙasashen na yammacin Afurka.
Wannan lamari dai yasa ƴan adawa da gwamnatin ke cewa dama Bazoum kwatar mulki yayi ba zaɓarsa talakawa suka yi ba.
Da yake martani game wanna batu, kakakin Jam’iyya PNDS Tarayya Alhaji Asmana Muhammadu yace wannan lamari ba haka yake ba, “Shugaban ƙasa baya tsoron kowa, ni na sanshi sakarata 30 tare da shi, bayan Allah babu wanda yake tsoro tun da ma, ballentana yanzu da ya zama shugaban ƙasa”.
Ce-ce kucen dai ya samo asaline bayan da wata jarida ta ƙasar Kanada ta wallafa cewa, shugaban ƙasar Nijar Muhammadu Bazoum ya ƙauracewa kwana a gidan Gwamnati, tun lokacin da sojoji suka kifar da Gwamnatin ƙasar Burkina Faso.
You must be logged in to post a comment Login