Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ban Saci Kudaden Nijeriya ba- Emefiele

Published

on

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya musanta zarge-zargen satar dukiyar ƙasa da ake yi masa a wani rahoton Mai Bincike na Musamman kan harkokin bankin CBN da aka fitar a baya-bayan nan.

Ya bayyana matsayin nasa ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Re: Emefiele, others stole billions, illegally kept Nigeria’s funds in foreign banks’ da ya fitar ranar Lahadi.

Idan za ku iya tunawa a cikin makon jiya ne, Mai Bincike na Musamman kan harkokin Babban Bankin Najeriya, Jim Obaze, ya bankaɗo cewa tsohon gwamnan bankin ya jibge fam miliyan 543, 482,213 ba tare da izini ba a bankunan Birtaniya kawai.

Bbc ta ruwaito cewa, Godwin Emefiele ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ya ce, bayan sakin sa a matakin beli daga gidan yarin Kuje, hankalinsa ya kai kan wasu labarai masu alaƙa da rahoton Jim Obaze.

“Na karanta labaran, kuma da ƙarfin murya ina cewa abin da suka ƙunsa, ƙarairayi ne da karkatar da hankali da kuma maƙarƙashiya don a ɓata min suna, a ci mini zarafi sannan da biyan muradin mai binciken.”

Ya kuma ce ba shi da hannu a buɗe asusun ajiya 593 a sassan duniya, kuma bai ma san an buɗe su ba.

Sai dai ya ce akwai sashe-sashe na babban bankin da ke da iko su aiwatar da irin waɗannan harkoki kamar yadda doka ta amince musu bisa tanade-tanaden aikin CBN.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!