Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ban taya Ɗanzago murnar zama shugaban jam’iyya ba – Buhari

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya musanta nuna goyon bayansa ga kowane tsagin shugabacin jam’iyyar APC na Kano.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ya ce Buhari bai taya wani ɓangaren jam’iyyar murnar samun shugabanci ba.

Ya ci gaba da cewa, jam’iyyar APC na ci gaba da ƙoƙarin samar da haɗin kai tsakanin magoya bayanta, saboda haka ba zai goyi bayan wani ɓangare ba, musamman kasancewar lamarin ya kai gaban kotu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Shugaban jam’iyyar tsagin tsohon Gwamna Shekarau, Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya shaida wa BBC Hausa cewa Buhari ya taya shi murna.

A Jumu’ar nan ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, sannan daga bisani rahotanni suka ce ya gana da Alhaji Ahmadu Haruna Zago.

A watan Oktoban da ya gabata ne rikicin jam’iyyar APC a Kano yayi ƙamari bayan zaɓen shugabanci biyu da aka yi.

Tsagin Gwamna Ganduje ya sanar da zaɓen Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, yayin da tsagin tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya zaɓi Alhaji Ahmadu Haruna Ɗanzago.

Sai dai a watan Nuwamba uwar jam’iyyar ta ƙasa ta aiko da kwamiti domin yin sulhu, wanda kuma abin ya faskara.

Kwamitin ya zauna da dukkan ɓangarorin biyu amma ba a cimma matsaya ba.

A ƙarshen watan Nuwamban ne wata kotu a birnin tarayya Abuja ta rushe zaɓen shugabancin mazaɓu da Gwamna yayi, inda ta tabbatar da na tsagin Malam Shekarau.

Tsagin Gwamna sun garzaya kotun domin neman ta rushe hukuncin amma ba ta amince ba, sai ma ta sake tabbatar da hukuncin ta na baya.

A gefe guda uwar jam’iyyar ta APC wadda ita ce aka yi ƙara, ta ce bata karɓi kwafin takardar hukuncin kotun ba.

Yanzu dai al’umma sun zuba idanu domin kallon yadda wannan shari’a zata ci gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!