Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Bankin duniya zai inganta fannin abinci ta hanyar zuba jarin dala biliyan 10 a Afrika

Published

on

  • Shugaban Bankin Akinwumi Adeshina zai zuga jarin dala biliyan goma don farfado da fannin abinci a Afrika
  • Akinwumi Adeshina ya bayyana yayin taron daya gudana a kasar Senegal.
  • Yayi kira ga wadanda suka halarci taron da su tsara yadda za’abi a bunkasa fannin noma a kasashen Afrika.

Bankin raya kasashen Afrika zai zuba jarin dala biliyan 10 don mayar da Afrika cibiyar samarwa Duniya abinci.

Shugaban Bankin Akinwumi Adeshina ya bayyana wannan kudiri a wajen taron bunkasa aikin noma da samar da abincin da ke gudana a kasar Senegal, wanda ya samu halartar shugabannin kasashen Afirka da ministoci da kuma masana ayyukan noma da samar da abinci.

Akinwumi Adeshina ya yi kira ga shugabannin 34 da suka halarci taron tare da ministoci 70 da ‘yan kasuwa da manoma da shugabannin kamfanoni da su zakulo hanyoyin da za’a bi don inganta noma a Afirka.

Shugaban bankin ya ce za’a samu nasarar wannan manufa ne kawai idan an hada kai domin tafiyar bai daya dan bude kofofin arzikin da Allah ya wadata nahiyar da su.

Rahoton: Bara’atu Idris Garkuwa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!