Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tun yanzu an samu koma bayan tattalin arziki a Nigeriya: Abdul Turawa

Published

on

Masanin tattalin arzikin a jami’ar tarayya dake Dutsen jihar Jigawa Dakta Abdul Nasir Turawa Yola ya ce, ‘karancin hada-hadar kudi da aka samu a yan kwanakin nan sakamakon kusantowar wa’adin da babban bankin kasa CBN ya bayar na daina amfani da tsaffin kudi ya kawo ci baya ga tattalin arzikin Najeriya’.

Dakta Abdul Nasir Turawa Yola ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Wakiliyar mu Ummulkhairi Abubakar Ungogo.

Dakta Abdul Nasir ya kuma ce ‘wa’adin da CBN din ya bayar na watanni uku ka iya sanya dubban mutane asarar kudaden su wanda hakan zai shafi tattalin arzikin kasar nan kai tsaye’.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/01/LABARAN-RANA-NAIRA-ECONOMY-27-01-2023.mp3?_=1

Dakta Abdul Nasir Turawa Yola kenan masanin tattalin arziki a jami’ar tarayya dake Dutsen jihar Jigawa.

Rahoton:Abubakar Tijjani Rabi’u

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!