Connect with us

Labarai

Barau FC kungiyar Gwamna Abba da jihar Kano ce- Shitu Canji

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Barau FC ta koka bisa abinda ta kira yi mata kafar Ungulu dangane da basu damar buga wasannin su na kakar firimiyar NPFL ta Najeriya ta 2025/26 a filin wasa na Sani Abacha.

Shugaban kungiyar Alhaji Ibrahim Shitu Canji ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da kungiyar ta kira da ta bayyana cewar har yanzu an ki sahalewar tawagar buga wasannin ta a filin, kasa da mako guda da fara gasar.

“Mun yi duk abinda zamu yi na cika ka’idoji tare da amincewa da biyan kudi Naira Miliyan 10, duk da cewar a Kano muke bai kamata mu biya hakan ba amma an ce ba za a bamu damar buga wasanni ba sai mun biya kimanin Naira Miliyan 50 a cewar hukumar wasanni ta jihar Kano ‘Sport Commission”.

“Na tabbata duk abinda ake mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf bai sani ba , domin kungiyar Barau FC ta shi ce ta jihar Kano kuma Yana alfahari da ita kamar yadda yake da Kano Pillars, don haka muna kira ga re shi da ya duba tare da sa baki don bamu damar buga wasanni kafin kammala gyaran filin mu dake Dambatta” Inji Shitu Canji.

Shugaban na Barau ya kara da cewa tabbas Gwamna zai yi alfahari da kafa tarihi da barin Kyakyawar makoma a harkar wasanni wanda a Zamanin sa aka samu kungiyoyin firimiya biyu dake wakiltar Kano, tare da samar da dumbin aiyyuka ga al’umma da Matasa tare da kautar dasu daga shaye -shaye da rikicin Daba da fashin Waya.Don haka suna da yakinin in Gwamna ya san halin da suke ciki zai dau matakin gaggawa don bawa kungiyar dama ta buga wasannin ta a Sani Abacha a matsayin Barau FC, kungiyar sa ta biyu a Kano kana ta Al’ummar a jihar ba wai kawai Siyasa ko banbacin jam’iyya ba.

A baya dai rahotanni sun tabbatar da cewar hukumar wasanni ta jihar Kano tare da hukumar kwallon kafa sun amincewa tawagar ta Barau FC, buga wasannin ta na gida a filin na Sani Abacha a wani mataki na bata dama kafin kammala aikin filin wasan tawagar dake karamar hukumar Dambatta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!