Connect with us

Labarai

Pillars ta kadu kan tarar da LMC ya yi mata – Jambul

Published

on

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta ce tayi mamakin tarar da kamfanin shirya gasar League ta kasa LMC ya cita sakamakon hargitsin da ya faru a wasan ta da ta buga da Akwa United a ranar Lahadi 13 ga watan Yuni.

Shugaban kungiyar Alhaji Surajo Shu’aibu Yahya Jambul ne ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da ya karbi sakon tarar daga LMC.

“Mun yi matukar kaduwa a lokacin da muka fara jin rade-radin an ci tarar mu, kafin daga bisani a aiko mana da takaddar tarar, “ inji Jambul.

Ya kara da cewa, Pillars bata sayar da tikitin shiga filin wasan ga kowa ba, haka kuma bata san yadda aka yi wadanda suka tayar da hargitsin suka shiga cikin filin ba.

Jambul ya kuma ce, “Kasancewar mu masu bin doka da oda zamu cigaba da yin duk mai yiwuwa don ganin mun ciyar da gasar League da kuma wasan kwallon kafa gaba, amma dai ya kamata a rinka yin adalci a dukkan lamura.”

Ya kuma shawarci masu ruwa da tsaki kan harkokin wasannin da su yi nazari kan abinda ya faru a lokacin da kungiyar ta Pillars da kuma takwararta ta Akwa United ke buga wasan don samo daidaito game da kura-kuran da akan tafka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!