Labarai
Barayin da suka addabi Kwari ba ‘yan asalin Kano ba ne- SA
Mahukuntan kasuwar kantin kwari sun jan hankalin yan kasuwar da su yi taka tsan-tsaan da masu shigowa kasuwar don yin sayayya sakamakon adadin barayin da ake kamawa a kasuwar yana kara karuwa a kullum wanda da dama suke yo takakiya daga wasu jihohin domin su zo su yi sata a kasuwar.
Mai baiwa Gwamna shawara na musamman kan kasuwar kantin kwari, Alhaji Ibrahim Garba Kamfani, ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Freedom radio.
Ya kara da cewa ya zuwa yanzu sun kama mutane da dama wanda yawancin su ba ‘yan kano bane da suke shigowa kasuwar a kungiyance inda akafi kama mata da wannan mummunar dabi’a
Ibrahim Garba Kamfani, ya kara da cewa kwamitin tsaron kasuwar kantin kwari zai cigaba da saka ido kan shige da ficen mutane a kasuwa domin dakile wadan nan bata garin babu dare ba rana.
A wannan lokacin duk wanda suka kama ba a saurara masa ba za a tabbatar hukunci yayi aiki akan sa domin ya zama darasi gama su son yin irin wannan.
You must be logged in to post a comment Login