Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kayan masarufi sun fara sauka sakamakon faduwar farashin Dala

Published

on

Yan kasuwa a kasuwar kayan masarufi a jihar Kano sun baiwa al’umma tabbacin samun saukin farashn kayan masarufi da zarar tsohon kayan da suke da shi ya kare, sakamakon duk da tsohon farashin Dala Amurka aka saye su.

Mai Magana da yawun kasuwar Singa da kewaye, Alhaji Bashir Madara ne ya bayyana hakan yayin tattaunawar sa da Freedom radio.

Bashir Madara ya kara da cewa tuni wasu daga cikin kayayyakin masarufi da ake sayarwa a kasuwar farshin su ya sauka musamman ma wanda ake siyowa daga kamfanoni irin su shikafar waje da taliyar yara da taliya da sabulun wanki dana wanka.

Ya kara da cewa wanda da basu sakko ba sune wanda ake sayan su da tsohon farashin Dala da kuma irin shinkafar gida sakamakon samfarerarta da take wahala.

Alhaji Bashir Madara ya cewa da dama daga cikin yan kasuwa a yanzu sun tura oda da wannan sabon farashin dala kuma da zarar kayan sun zo saukin zai linka na yanzu ma.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!