Labarai
Barazanar yajin aiki: an cimma matsaya tsakanin ƙungiyar JUHESU da gwamnatin tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce ta cimma matsaya da gamayyar ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya JUHESU kan barazanar su na tsunduma yajin aiki.
Ministan ƙwadago da samar da aikin yi Dakta Chris Ngige ne ya bayyana hakan, jim kaɗan bayan kammala tattaunawa da gamayyar ƙungiyar a ranar Talata na tsawon sa’o’i 5.
Ngige ya ce, dukkanin ɓangarorin biyu sun samu fahimtar juna, a don haka tattaunawar ta yi armashi, kuma za a sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a mako mai zuwa.
Gwamnatin tarayya za ta gana da JUHESU kan batun yajin aiki
A cewarsa, yarjejeniyar ta haɗa da inganta alawus-alawus da kuma duba shekarun ritaya daga shekaru 60 zuwa 65, sai kuma basussukan da ake bi na daidaita mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
Idan za a iya tunawa a ranar 3 ga watan Satumba JUHESU ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 15 kan ta biya musu bukatun su ko kuma su tsunduma yajin aiki.
You must be logged in to post a comment Login