Barka Da Hantsi
Barka da Hantsi: Tattaunawa kan dalilan da ke janyo haihuwar jariran da basu cika wata 9 ba
Ranar 17 ga watan Nuwambar kowace shekara, rana ce da hukumar lafiya ta majalisar ɗinkin duniya ta ware domin kula da lafiyar ‘Bakwaini’ a duniya wato ‘world premature day’.
An tattauna domin jin dalilai na kimiyyar lafiya da ka iya janyo haihuwar jariran da basu cika wata 9 ba da sauran batutuwa masu alaƙa da lafiyar ƙananan yara.
Baƙin sun haɗa da AbdulMalik Saminu, likitan yara a asibitin koyarwa na Aminu Kano da kuma Muhammad Abba Musa babban jami’in jinya a fannin kula da ƙananan yara na Asibitin AKTH ɗin.
You must be logged in to post a comment Login