Labaran Kano
Bawa mata ilimi na da muhimmanci sakamakon yawansu- Farfesa Aliyu Musa
Daga Shamsu Da’u
Mataimakin shugaban jami’ar Yusuf Maitama Sule yayi kira ga kungiyoyin tsofaffin dalibai da suyi hobbasa wajen taimakon karatun mata tare da samar da ingantancen yanayin koyo da koyarwa don magance kalubalen da ake fuskanta a kasar nan.
Farfesa Aliyu Musa ya bayyana hakan ne yayin gudanar da taron tsofaffin dalibai na makarantar sakandaren mata ta kwana dake karamar hukumar Kura.
Ya kuma kara da cewa mata ne ke da mafi yawan rinjaye a cikin al’umma ,don haka bai kamata al’ummar mu ta rike hannu tana ji tana gani jahilci ya kashe ta ba.
A nata jawabin shugabar kungiyar tsofaffin daliban makarantar Farfesa Binta Tijjani Jibril ta ce kungiyar tasu ta magance matsaloli da dama da makarantar ke fuskanta.
Shugaban kungiyar iyayen yara sunyi kira da gwamnati data kawo wa makarantar dauki.