Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Bayan binciken shekara goma an samar da waken da kwari basa ci

Published

on

Bayan shafe shekaru goma tana bincike cibiyar binciken harkokin noma ta jami’ar Ahmad Bello da ke Zaria da hadin gwiwar gidauniyar binciken harkokin gona ta Afrika wato AATF sun sun gano irin wake da baya bukatar feshi da da yawa.

 

Cibiyar ta kuma ce kwarin  da ke adabbar manoman wake baya yi masa illa wanda aka fi sani da kwarin maruca sun kammala bincike.

 

Wannan bincike dai an fara shi ne tun shekara 2009,a wani yunkurin tabbatar da abinci ya wadata a kasa baki daya.

 

Hakan ce ma ta baiwa cibiyar bincken harkokin noma IAR damar gudanar da binciken , tuni suka kammala kuma ake sa ran wannan irin zai wadata a kasuwa a watan Disamba mai zuwa.

 

Kamar yadda kasa ta bukata na tabbatar da abinci ya wadata  ne ma ya sa wannan cibiya da hadin gwiwar wasu cibiyoyi suka samar da wani irin wake da baya jimawa kafin ya fito sannan baya bukatar feshi kamar yadda suka bayyana.

 

Shi dai wannan wake an jirkita hallitarsa wanda yayi daidai da yanayin da muke da shi a yanzu, ko da kuwa an girbi waken za’a iya shuka wasu irin waken.

 

Da yake jawabi Farfesa Ishiyaku  wanda Dr Muhammad Lawan ya wakilce shi ,kuma jagora a wajen samar da irin ya ce ,sakamakon gwajin da suka gani a gonar Bagadawa abin a yaba ne.

 

Kuma sakamakon da suka samu a gonar da aka yi gwaji a jihar Kano , a garin na Bagadawa yayi daidai da sakamakon da suka samu a shekaru shida da suka gabata da suka gudanar da gwaje gwaje a jami’ar Ahmadu Bello.

 

Ya kara da cewa shi wannan sabon irin zai ba da yabanya ga manomi da Karin kimanin kaso 40 na yadda yake samu a da.

 

Ya ce wannan kuwa ya biyo bayan gwaje-gwajen da suka gudanar a jami’ar su da wasu gonaki wanda dukkanin sakamakon da suke samu ya tabbatar da hakan.

 

Bincike da suka shafe shekaru goma ya nuna cewar babu wani banbamci tsakanin waken da aka saba ci da wannan wake.

 

Daga karshe Shima wani jami’i a gidauniyar binciken harkokin noma ta Afrika AATF  Dr Issoufou Kollo, yace  binciken na cikin kudirin tabbatar da abinci ya wadata a nahiyar Afrika baki daya tare da shan alwashin tabbatar da hakan.

 

Ya ce babban dalilin da ya sa suka yi gwajen irin waken a garin Bagadawa shine don a nunawa manoma a zahirance abinda wannan wake yake yi.

 

Wasu daga cikin manoman da aka gudanar da gwajin a gonakin su , Malam Suleman Aliyu ya ce ya shafe shekaru 16 yana noman wake amma bai taba ganin yadda wake ya fito a kasa da kwanakin da suka saba  ba.

 

Yace ko kwaro daya bai ci wannan wake ba ,baya ga karancin feshin da suka yi a gonar ta su.

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!