Labarai
Bayan cikar wa’adi: Rashin sabunta lasisi zai hana direbobin adaidaita sahu hawa titi a Kano – KAROTA
Hukumar KAROTA a jihar Kano ta ce, daga ƙarshen watan Maris na 2022 za ta haramtawa duk direban adaidaita sahun da bai sabunta lasisinsa ba hawa kan titi.
Mai baiwa gwmana shawara kan harkokin hukumar KAROTA Alhaji Nasir Usman Na’ibawa ne ya bayyana haka ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.
Shirin ya mayar da hankali kan matakin da hukumar zata dauka kan duk direban adaidaita sahun da bai sabunta lasisinsa ba.
“Tun a ƙarshen watan Fabrairu wa’adin da aka cimma tsakanin hukumar KAROTA da ƙungiyoyin direbobin adaida sahun ya cika, amma kuma mun ƙara musu wa’adi ne domin ganin halin da ake ciki a yanzu” a cewar Na’ibawa.
Ya ci gaba da cewa “Yanzu mun sanya wa’adin makonni uku ga direbobin na su sabunta lasisin su ko kuma mu hana su hawa kan titinan jihar Kano baki ɗaya”.
A watan Janairun 2022 ne matuƙa baburan adaidaita sahu a Kano suka shiga yajin aikin kwanaki uku kan batun sabunta lasisi, lamarin da ya gurgunta harkokin sufuri a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login