Labarai
Bayan juyin mulki, sojoji sun kame shugaban Guinea
Sojojin Guinea a yau Lahadi 05 ga watan Satumbar shekarar 2021 sun ce sun karbe ikon gwamnati tare da dakatar da Tsarin Mulki.
Kanal Mamady Doumbouya na sojojin Guinea ya fada a wani faifan bidiyo da aka dauka a Conakry babban birnin kasar cewa an rusa majalisar dokokin kasar.
Wani bidiyo kuma ya bazu a kafafen sada zumunta wanda ke nuna shugaba Alpha Conde yana tsare da sojoji. Daga baya aka tura shi cikin mota aka kore shi.
Kasar Guinea bata shirya fafatawa da Nigeria ba
Wannan ci gaban ya zo ne bayan da mazauna yankin suka ji karar harbe -harbe na sa’o’i biyu a fadin babban birnin kasar.
Mista Doumbouya ya ce an rufe dukkan hanyoyin kasa da na sama a cikin wucin gadi, inda ya nemi ‘yan kasar da su kasance a gida.
Mista Doumbouya ya kuma koka da cin hanci da rashawa da talauci a matsayin manyan dalilan karbe mulkin, yana mai cewa Mista Conde ya gaza cika alkawuran da ya yi wa mutanen Guinea.
Mista Conde mai shekaru 83, ya lashe wa’adin mulki na uku a watan Oktoban da ya gabata.
You must be logged in to post a comment Login