Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Majalisar Malaman Kano ta yi zargin ana shirya mata makirci

Published

on

Majalisar malamai ta ƙasa reshen jihar Kano ta yi Alla-wadai da yunƙurin wasu malamai na shirya maƙarƙashiyar tunɓuke shugabanta Malam Ibrahim Khalil.

Hakan na cikin wata sanarwar bayan taro da Mataimakin Babban Sakataren Majalisar Farfesa Muhammad Babangida Muhammad ya aike wa Freedom Radio a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce, “Malamai sun kaɗu matuƙa game da wani motsi ta ƙarƙashin ƙasa da wasu bara-gurbin malamai ke yi, domin haddasa rikici da rarrabuwar kan majalisar”.

Ƙarin labarai:

Muƙabalar malamai 6 da aka taɓa karawa a tsakanin malaman Kano

Malaman islamiyya sun yi Alkunutu a Kano

Malaman sun kuma bayyana takaicinsu kan yadda wasu malamai ke zubar da ƙimarsu ga ƴan siyasa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, Malaman Kano daga ƙananan hukumomi 44 sun jaddada mubaya’arsu ga shugaban majalisar Malam Ibrahim Khalil.

Sannan majalisar ta yi kira ga musulmai da su kasance a farke, kan duk wani makirci da ake shiryawa majalisar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!