Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bayan sauke Dan Sarauniya, Ganduje ya nada sabon kwamishina

Published

on

Da safiyar Larabar nan ne gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabon kwamishina Idris Garba Unguwar Rimi da zai kasance daya daga cikin mambobin majalisar zartarwar na jihar Kano.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce hakan ya biyo bayan kokarin da ake yi na cike gurbi daya da aka rasa na wani kwamishina a kwanakin baya.

Sai dai yace nan gaba kadan za a bayyana ma’aikatar da sabon kwamishinan zai rike

Da yake jawabi sabon kwamishinan da aka rantsar wanda a yanzu ake dakon jin ma’aikatar da zai rike Idris Garba Unguwar Rimi ya ce zai yi kokari wajen ganin jihar Kano ta samu cigaba

Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa sabon kwamishinan ya taba zama shugaban karamar hukumar Tofa da kuma kwamishina na kimiyya da fasaha anan jihar Kano.

Idan zaku iya tunawa a watan Afrilun da ya gabata ne gwamnan Kano ya sauke kwamishinan ayyuka na jihar Engr. Mu’azu Magaji Dan Sarauniya bayan wasu kalamai da yayi a shafinsa na Facebook kan marigayi Abba Kyari shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Sai dai daga baya Dan Sarauniya ya musanta tare da neman afuwa.

Karin labarai:

Ganduje ya tsige kwamishina bisa rubutu da ya yi a facebook

Da dumi-dumi : Ganduje ya kori kwamishinan ayyuka kan kalaman da ya yi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!