Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bayyana sirri a tsakanin ma’aurata shi ke kawo sakin aure – Hauwa Hussain

Published

on

Kungiyar yaki da cin zarafin ‘ya’ya mata da kananan yara ta kasa rashin jihar kano, ta bayyana cewar babban abinda ke haifar da matsalar aure  a kasar nan shine bayyana sirrin juna tare da shigowar mutanan da basu da hurumi cikin zamantakewar ke kara kawo yawaitar matsalar.

Shugabar kungiyar Hajiya Hauwa Hussain ta bayyana hakan ne jin kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan freedom radiyo wanda ya maida hankali kan yadda zamantakewar aure tatabarbare tare hanyoyin magance matsalar.

Hauwa Husain ta kuma ce kamata yayi ma’aurata a kasar nan su kasance masu hakuri da junan su tare rike sirrin su dan ganin a masu daidaito a tsakanin ma’aurata.

Koyi da bakin al’adu shi ke kawo mutuwar aure a Najeriya

Da yake bayani ta cikin shirin na Barka da hantsi Tijjani Muhammad Musa cewa yai rashin wayar da kan da ‘ya’ya mata da maza dabarun zaman aure lokacin aure ke kara gurbacewar zamantakewar aure a kasar nan.

Bakin sun bukaci ma’aurata da su kasance masu sauke nauyin da ke kan su, tare da kyautatawa juna dan ganin an samu zaman lafiya a gidajan aure.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!