Labarai
Bello Turji ya saki fiye da mutane 100 da ya ke tsare da su

Jagoran ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara Bello Turji, ya saki mutum sama da 100 da yake tsare da su a wani sabon yunkuri na samar da zaman lafiya da kawo karshen tashin hankali a jihar, da sakin ya biyo bayan dogon tsarin tattaunawa da amincewa da shirin sulhu da ake gudanarwa a wasu yankunan Arewa maso Yamma.
Shafin X, na Zagazola Makama kwararre kan harkokin tsaro ya wallafa cewa wadanda aka sako sun hada da maza, mata da yara, kuma an mika su ga hukumomin yankin kafin kai su asibiti domin binciken lafiya da kulawa.
Wata majiya da ta shiga cikin tattaunawar ta bayyana cewa an fara sakin mutane 36, sannan daga baya aka kara sakin wasu takwas, wanda ya kai jimillar 46 a matakin farko.
Daga baya kuma aka ci gaba da sakin sauran, har adadin da aka sako ya kai sama da mutum 100 baki daya, da majiyar ta kara da cewa ana sa ran karin sakin mutane cikin kwanaki masu zuwa yayin da tattaunawa ke ci gaba.
You must be logged in to post a comment Login