Labaran Kano
Bidiyon Dala: Ganduje ya biya Ja’afar Ja’afar N800,000 saboda ɓata masa lokaci
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya biya ɗan jaridar nan Ja’afar Ja’afar Naira dubu ɗari takwas saboda ɓata masa lokaci.
A ranar Juma’ar nan ne Ja’afar Ja’afar ya shaida wa Freedom Radio cewa, Gwamnan ya biya shi dubu ɗari takwas kamar yadda kotu ta umarce shi.
A watan Yulin wannan shekara ne Babbar Kotun Kano mai lamba 9 da ke unguwar Bompai ƙarƙashin mai shari’a Sulaiman Baba Na Malam ta umarci Gwamnan ya biya Ja’afar Ja’afar da kanfaminsa kuɗin, saboda ɓata masa lokaci da yayi wajen shari’a.
An shafe shekaru huɗu ana fafata shari’a tsakanin Ja’afar da Gwamnan bayan da ya fitar da wasu faya-fayan bidiyo da ya nuna zargin Gwamnan da sunƙuma dalolin Amurka a aljihu.
Sai dai a watan Mayun wannan shekara ɗan jarida Ja’afar Ja’afar ya fice daga Najeriya zuwa birnin Landan.
Hakan ya biyo bayan zargin baraza da rayuwarsa da ya yiwa Gwamnatin Kano, bayan da Gwamna Ganduje ya musanta sahihancin bidiyon Dalar a wata hira da BBC Hausa.
You must be logged in to post a comment Login