Labarai
Biyayyar Baffa Babba Danagundi ce ta sa ya amince da dakatarwar da gwamnati ta yi masa – S.A KAROTA
Mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin hukumar KAROTA Nasiru Usman Na’ibawa ya ce, Baffa Babba Danagundi ya amince da dakatarwar da gwamnati ta yi masa ne saboda biyayyarsa.
Nasiru Usman Na’ibawa ya bayyana hakan ga Freedom Radio jim kadan bayan da gwamnatin Kano ta dakatar da Baffa Babba Danagundi daga yunkurin ajiye mukaminsa.
Mataimakin gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna shi ne ya dakatar da yunkurin na Baffa a madadin gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje wanda a halin yanzu baya gari.
“Sanin kowa ne Baffa yana yin biyayya ga mai girma gwamna wanda hakan ne ya sanya da gwamnati taki karbar takardar ajiye aikin sa kuma ya amince”.
“Ofishin mataimakin gwamna ya sanar da mu cewa a dakata da maganar ajiye aiki zuwa wani lokaci don haka za mu jira zuwa lokacin da suka dauka” a cewar Na’ibawa.
A yau litinin ne dai rahotanni suka tabbatar da cewa Baffa Babba Danagundi zai mika takardar ajiye aiki, domin samun damar yin takara a kakar zaben 2023, kamar yadda sabuwar dokar zabe ta tsara.
You must be logged in to post a comment Login