Kasuwanci
Borno ta fara fitar da kayayyakin robobi zuwa ƙasashen duniya- Gwamna Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa, jiharsa ta fara fitar da kayayyakin robobi zuwa ƙasashen duniya.
Gwamnan, ya bayyana hakan a matsayin gagarumin ci gaba da ke nuna yadda gwamnati ke himmatuwa wajen farfaɗo da masana’antu da bunkasa tattalin arzikin jihar.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara masana’antar robobi ta jihar, inda ya ce, wannan nasara ta samo asali ne daga ƙoƙarin gwamnati na tallafa wa masana’antu domin rage dogaro da kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashen waje.
Haka kuma ya ce, fitar da kayayyakin da aka sarrafa a cikin gida zai buɗe sabbin damammaki ga matasa, musamman ta fuskar samar da ayyukan yi da ƙara wa tattalin arzikin jihar kuɗin shiga.
You must be logged in to post a comment Login