Kiwon Lafiya
Boss Mustapha ya bayyana tsaikon da aka samu na mika rahoton rikicin inshorar lafiya
Babban sakataren gwamnatin taraya Boss Mustapha ya kare tsaikon da aka samu na mika rahoton kwamitin bincike kan musababin rikici a hukumar dake kula da Inshorar lafiya ta kasa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa.
Haka zalika shugaban kasar ya kafa kwamitin ne don bincikar zargin da ake wa babban sakatare a hukumar Inshrara lafiy ta kasa farfesa Usman Yusuf kan yin almundahar kudaden.
A yayin da yake karabar rahoton daga Kwamitin mutum 7, Boss Mustapha ya ce akwai bukatar gudanar da bincike mai zurfi a hukumar ta NHIS wanda ya sanya kwamitin ya kwashe makwanni 7 yana gudanar da bincike akai mai makwan makwanni 2 da gwamnatin tarayya ta bashi.
Haka zalika Boss Mustapha ya ce gwamnatin tarayya ta damu matuka kan rikicin hukumar ta NHIS,wanda ya sanya har ta kai ga dakatar da babban sakataren hukumar farfesa Usman Yusuf.