Labarai
Bouna Sarr ya amince ya wakilci kasar Senegal

Dan wasan tawagar Bayern Munich , Bouna Sarr ya amince ya wakilci kasar Senegal a karo na farko bayan da a baya ya kaucewa haka.
Mai shekaru 29, Saar zai wakilci kasar ta Senegal a wasannin da zata fafata a watan Oktoba na 2021, na neman tikitin zuwa gasar cin Kofin Duniya na 2002 a kasar Qatar.
Dan wasan na da damar wakiltar kasashen Senegal da Guinea sai kasar Faransa , kasancewar bai taba wakiltar daya daga cikin kasashen ba a wasa na Babbar tawagar kasa.
You must be logged in to post a comment Login