Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Brazil na tattaunawa da PSG akan dan wasa Neymar

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta kasar Brazil, CBF, ta fara tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain, don cimma matsayar dan wasan ya jagoranci tawagar kasar a gasar wasannin motsa jiki na bazara wato Olympic a birnin Tokyo na kasar Japanda zai gudana a shekarar bana.

Dan wasa Neymar,  na daga cikin tawagar kasar sa a matsayin ‘yan wasa guda uku da aka kayyade shekarun sun da suka haura ashirin da uku da ake bada dama ga kasashe da su yi amfani dasu a cikin tawagar su da suka wakilci kasar Brazil a gasar da  a ka kammala a birnin  Rio na kasar Brazil shekarar 2016, wanda Brazil suka dauki lambar zinare.

Labarai masu alaka

An sayi dan wasan Dambe naira dubu hudu a Kano

Za’a kece raini tsakanin Man City da Madrid

 

Dan wasa Neymar, ya nuna sha’awar sa ta wakiltar kasar sa a gasar cin kofin nahiyar Amurka wato Copa America, da zai gudana a kasar Columbia, da ga ranar sha biyun ga watan yuni a kuma karkare sha biyu ga watan yuli, wanda da zarar an kammala shi zai zama  kwana goma tsakanin su da fara gasar wasannin Olympic.

‘Yan wasa da suka hada da Vinicius Junior da Rodrygo da  Reinier da sabon dan wasan kungiyar Lyon ta kasar Faransa,   Bruno Guimarães  na daga cikin ‘yan wasan da ake sa ran zasu wakilci Brazil a gasar.

 

Kasashe  goma sha shida, 16 , ne zasu fafata a wasan kwallon kafa na maza, har da mai masaukin baki kasar  Japan.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!