Labarai
Bude iyakar Nijeriya cigaba ne ga kasuwanci kasar-‘Yan kasuwa
Al’amura sun fara komawa dai-dai a wasu iyakokin kasar nan bayan da gwamnatin tarayya ta amince a riga shigo da wasu nau’ikan kayyayaki cikin kasar nan.
Al’ummar dake kan iyakar Nigeria da Janhuriyar Niger a Yankin Jibiya a jihar Katsina sunce sun fara samun saukin lamura a bangaren sana’ar su ta fitowa da kayayyaki daga Janhuriyar Niger bayan da Mahukunta a Kasar nan suka amince a rika shigowa da wasu nau’in kayayyaki.
Wasu daga cikin wadanda suke gudanar da kasuwanci a iyakar sun bayyanawa Freedom Radio radio ‘cewa a iya ‘dan takaitaccen lokacin nan da mahukunta suka bayar da dama a shigo da Aya da Dabino da alewa da atamfar da wake sun samu cigaban kasuwancin su fiye da misali’.
Sai dai kuma wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun ce ‘akwai bukatar a Kara bada dama a rinka shigo da kayan masarufi, don bunkasar kasuwanci dama tattalin arziki kasar nan’.
Rahoton: Yusuf Ibrahim Jargaba
You must be logged in to post a comment Login