Kowane Gauta
Bude iyakokin kasa na tsandauri shi ne kadai mafita – Danjuma Bakin Wafa
Adamu Dan juma’a Isa Bakin wafa daga jam’iyyar APC ya shawarci gwamnatin Shugaba Buhari data bude iyakokin Najeria na tsandauri domin zai ragewa ‘yan kasa matsin tattalin arziki da suke fama dashi a halin yanzu.
Danjuma Isa bakin wafa ya bayyana haka ne ta cikin shirin Kowane Gauta na Freedom Radio, yana mai cewa talakawan Najeria na cikin wani hali a yanzu don haka bai kyautu ace ana samun matsala a gwamnatin APC ba.
Danjuma Isa ya kara da cewa, “Ya zama wajibi shugaban kasa ya rika bibiyar ayyukan da ya bayar kasancewar rashin bibiya ne yasa al’ummar kasar nan ke fuskantar matsaloli daban-daban”.
You must be logged in to post a comment Login