Kiwon Lafiya
Buhari: gwamnatinsa ba zata kyale masu hannu a rikicin jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna ba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ba za ta kyale duk wani da aka samu yana da hannu wajen rasa rayukan al’umma a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da ma sauran sassan kasar nan ba.
Muhammadu Buhari ya kuma yi Allawadai da ayyukan batagari a jihohin, inda ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar da cewa sun dakile ayyukan ‘yan bindiga.
Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai tare da rakiyar jamia’n tsaro a kauyukan ‘Yar Santa da kuma Tsamiyar Jino a yankin karamar hukumar Kankara.
Gwamna Aminu Bello Masari ya ce ya kai ziyara kauyukan ne domin yin jaje ga al’ummar kauyukan biyu game da rashin tsaro da ke addabar yankunan su.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimakin na musamman ga gwamna Aminu Bello Masari kan harkokin yada labarai Abdu Labaran Malumfashi, ta ce, nan gaba ba da dadewa ba, za a kawo karshen ayyukan batagari.