Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Buhari zai dakatar da yajin aikin likitoci a Najeriya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce ta shirya tsaf don dakatar da yajin aikin da likitoci masu neman kwarewa suke yi da kuma shirin da ma’aikan lafiya ke yi na tsunduma yajin aiki.

Ana sanya ran Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Dr. Chris Ngige da Ministar kudi Zainab Ahmad da kuma ministan Lafiya Dr. Osagie Ehanire zasu yi wani zama a yau da shugabannin kungiyar likitoci ta kasa kan batun.

Tawagar ministocin za kuma ta tattauna da kungiyar ma’aikatan lafiya ta kasa a gobe Alhamis don lalubo hanyar dakatar da yajin aikin da suka shirya tafiya a makon da ya gabata.

A cewar ministan kwadago Chris Ngige gwamnatin tarayya zata yi duk mai yiwuwa wajen dakatar da yajin aikin nasu don kuwa ba zata zuba idanu yajin aikin nasu ya janyo rufe asibitocin kasar nan ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!