Labarai
Buhari na jagorantar taro kan sha’anin tsaro
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na jogarantar taron majalisar ƙoli kan sha’anin tsaro a fadar sa da ke birnin tarayya Abuja.
Daga cikin wadanda suka halarci taron sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
Sai mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da babban hafsan tsaron ƙasar nan Janar Lucky Irabor.
Sauran sun haɗar da shugaban hafsan soji da na ruwa da kuma babban Hafsan sojin sama, sai sufeto janar na ƴan sanda Usman Baba Alƙali.
Kafin a fara taron sai da shugaba Buhari ya yi wa Laftanar Kanar Yusuf Mukhtar Dodo ado da sabon mukaminsa na Kanar a ranar Alhamis 25 Nuwambar 2021.
You must be logged in to post a comment Login