Labarai
Buhari ya ce ya zama wajibi Najeriya ta ciyo bashi daga kasashen waje

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnatin sa ta rika ciyo bashi daga kasashen ketare matukar ana son a magance matsalar da kasar nan ke fama da shi.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kwamitin bayar da shawara kan tattalin arziki a birnin tarayya Abuja jiya Talata.
Har ila yau, Muhammadu Buhari ya ce, ciyo bashin kudaden zai taimaka wajen samar da titina a kasar nan da samar da layukan dogo wanda za su taimaka wajen ceto da rayuwar al’ummar kasar nan daga fadawa cikin mawuyacin hali.
Shugaba Buhari y ace babu abinda al’ummar kasar nan a yanzu ke fatan samu sama da ayyukan raya kasa da zai kara bunkasa tattalin arzikin kasa.
You must be logged in to post a comment Login