Labarai
Buhari ya ciyo bashin sama da naira tiriliyan ɗaya daga ƙasar China cikin shekaru 6 -DMO
Wani rahoto daga ofishin kula da basuka na ƙasa DMO ya ce cikin shekaru 6 da suka gabata, gwamnatin shugaba Buhari ta ciyo bashin dala biliyan biyu da miliyan biyu daga ƙasar China.
Rahoton ya bayyana cewa ƙididdigar basukan da ake bin Najeriya ya zuwa ƙarshen watan yunin shekarar 2015, ya tsaya ne akan dala biliyan ɗaya da miliyan talatin da takwas.
Yayin da ya zuwa ranar talatin da ɗaya ga watan Maris basukan da ƙasar China ke bin Najeriya ya kai dala biliyan uku da miliyan arba’in.
A cewar ofishin na DMO basukan da ake karɓa daga China yana da kuɗin ruwa na kaso biyu da ɗigo hamsin, kuma za a biya ne cikin wa’adin shekaru ashirin.
You must be logged in to post a comment Login