Labarai
Buhari zai dauki matakan tsuke bakin Aljihu
A wani mataki da ake gani yunkuri ne na rage kudade da gwamnati ke kashewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da fitar da wasu sababbin ka’idoji ga ministoci da ma’aikatu da sassan gwamnati game tafiye-tafiye da su ke yi zuwa kasashen ketare.
A cikin wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya fitar a jiya Laraba, ta ce, wajibi ne ga dukkanin ma’aikatu da sassa da kuma hukumomin gwamnati da su mika da bayanan ziyara kasashen ketare da za su yi a shekara mai zuwa ga ofishin sakataren gwamnatin tarayya da kuma ofishin shugaban ma’aikatan tarayya.
Sanarwar ta ce dole ne ya kasance ministoci da ma’aikatu da sassa da kuma hukumomin gwamnati sun mika da bayanan a cikin zangon farko na shekara mai zuwa, kafin a fara aitawatarwa.
Buhari yayi ganawar sirri da Jonathan
Shugaba Buhari ya bukaci a baiwa ‘yan Najeriya mazauna Africa ta kudu kariya
Abunda ya kamata ku sani kan kasafin kudin badi
Haka zalika ta cikin sanarwar ofishin na sakataren gwamnatin tarayya ya ce, wajibi ne dukkan nin tafiye-tafiye na cikin gida ne ko na ketare wanda za a yi amfani da kudaden gwamnati ya kasance aikin da ya shafi gwamnati za a yi sannan a ba da hujjoji na kundin bayanai.
A cewar sanarwar gwamnati ta kuma haramtawa ministoci ko manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnati ko sauran shugabanni sassa da hukumomin gwamnati yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje sama da guda biyu cikin watanni hudu, sai dai in da umarnin shugaban kasa.
Haka kuma sanarwar ta yi gargadin cewa, babu wani minista da zai yi tafiya zuwa kasashen ketare da tawaga sama da mutum hudu ciki kuwa har da darakta da ke kula da bangaren da ministan zai kai ziyara akai.