Labarai
Buhari ya dawo gida bayan halartar taron majalisar ɗinkin duniya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Birinin tarayya Abuja litinin ɗin nan.
Shugaban ya dawo gida bayan shafe kimanin mako guda a babban taron zauren majisar dinkin duniya Karo na 76 da ya gudana a New York na Amurka.
Muhammadu Buhari ya sauka a Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, inda ya shiga jerin gwanon motocinsa zuwa fadar Aso rock da ke Villa.
A Yayin da yake jawabi a taron na majalisar dinkin duniya, Shugaba Bahuri ya bukaci zauran majalisar da ya kawo karshen wariyar launin fata da ake nunawa ƴan Afurka a duniya.
You must be logged in to post a comment Login