Labaran Kano
Buhari ya gana da Sarki Salman
Shugaban kasa muhammadu Buhari ya gana da Sarki Salman Bin Abdul’aziz na Saudi Arabia jiya a birnin Riyadh, inda kasashen biyu suka amince da kulla yarjejeniyar hakowa da kasuwancin Man Fetur da Iskar Gas a tsakaninsu.
Babban mataimakin na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya sanar da cewa shugabannin biyu Sun gana
ne a daidai lokacin da shiga kwana na biyu da fara taron tattalin arziki da Saudi Arabia ke jagoranta.
Ya kuma kara da cewa shugabannin biyu sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban kasashen biyu, baya ga man fetur da gas, wanda Najeriya da Saudi Arabia ke kan gaba wajen samar da su a duniya.
A don haka ne ma Sarki Salman ya alkawarta zuba jari a fannin Man Fetur da Gas din kasar nan tare da karfafa alaka tsakanin kamfanin mai na kasa NNPC da na Saudi Arabia Aramco.
Malam Garba Shehu ya bayyana cewa Shugaba Buhari daSarki Salman sun kuma tatauna kan al’amuran da suka shafi tsaro da suka kasashen biyu da
ma duniya baki-daya, tare da fatan magance kalubalen da fannin tsaron ke fuskanta.
Sannan kuma sun tattauna kan batun ilimi da kimiyya da fasaha da harkokin noma, don ganin yadda kasashen biyu za su mori juna a kai, noma, don ganin yadda kasashen biyu za su mori juna a kai.