Labarai
Buhari ya kara wa’adin wata daya don hada layukan tarho da lambar NIN
Gwamnatin tarayya ta kara wa’adin wata guda don ci gaba da yin rajistar hada layin dan kasa (NIN) da kuma layukan wayar tarho.
A baya dai gwamnatin ta ware wa’adin shida ga wannan wata na Afrilu a matsayin ranar karshe da za a gama aikin hada layukan wayar da lambar dan kasa (NIN), to sai dai yanzu an kara wa’adin zuwa ranar shida ga watan gobe na Mayu.
Ministan sadarwa da bunkasa fasahar tattalin arziki, Dr Isa Ali Pantami ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.
Ya ce tuni ma’aikatar ta aikewa shugaba Buhari da bukatar neman karin wa’adin kuma shugaban kasar ya amince da hakan.
A cewar sa ya zuwa yanzu, an samu ci gaba sosai wajen hada layukan na waya da lambar dan kasa, inda mutane akalla miliyan biyu da dubu dari shida suke hada layukansu da lambar dan kasa (NIN) a duk wata.
You must be logged in to post a comment Login