Coronavirus
Buhari ya rufe Kano ruf har zuwa mako biyu saboda Corona

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada umarni a rufe jihar Kano har tsawon makwanni biyu domin dakile cutar Corona a Kano da ma kasa baki daya.
Muhammad Buhari, ya bayyana hakan ne yau ta cikin jawabin sa da ya gabatar a gidan talabijin na kasa kan cutar ta Covid-19.
Ya ce” Na bada umarnin nan take a rufe jihar Kano har tsawon mako biyu. Domin haka gwamnatin tarayya za ta tallafa da dukannin abubuwan da a ke bukata na rayuwa da kuma kayan aiki, saboda a dakile cutar baki daya daga yaduwwar ta Kano zuwa makwabtakan jihohi”. A cewar Buhar.
You must be logged in to post a comment Login