Connect with us

Labarai

Buhari- Ya sauyawa manyan sakatarori 5 guraren aiki

Published

on

Gwamnatin tarayya ta sauyawa wasu manyan sakatarorin gwamnatin 5 guraren aiki.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da hakan, ta cikin wata sanarwar da shugabar ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Dakta Folasade Yemi-Esan, ta fitar ga manema labarai a daren ranar Juma’a 24 ga watan Satumbar shekarar 2021.

Buhari zai sake ciyo bashin sama da Dala biliyan 4

Manyan sakatarorin da aka sauyawa guraren aikin sun hadar da William Nwankwo Alo daga Ma’aikatar Lantarki zuwa hukumar ‘Yan Sanda (PSC) da Abel Olumuyiwa Enitan daga Ma’aikatar Muhalli zuwa Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama sai Hassan Musa daga Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama zuwa Ma’aikatar Muhalli ta kasa.

Sauran sun hadar da Nebeolisa Anako daga Ma’aikatar Matasa da wasanni zuwa Ma’aikatar Wutar Lantarki sai kuma Ismaila Abubakar, daga ma’aikatar tsaro ta ‘yan sanda zuwa Ma’aikatar Matasa da wasanni.

Sanarwar ta ce canjin wuraren aikin  ya fara aiki nan  take.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!