Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Buhari ya shaida ɗaurin auren ɗan sa a Kano

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya shaida ɗaurin auren ɗan sa Yusuf Buhari da ƴar gidan sarkin Bichi Zahra Bayero.

Shugaba Buhari ya sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano bayan ya halarci jihar Adamawa duk a wannan rana.

Jim kadan bayan saukar sa ya samu tarba daga gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Rahotanni sun bayyana cewa, an daura auren na su jim kadan bayan sakkowa daga masallacin juma’a, kuma Mamman Daura shi ne ya kasance waliyyin Ango, sai Aminu Dantata da ya kasance waliyyin Amarya.

Daurin auren ya samu halartar gwamnoni da ministoci da sauran manyan yan siyasar ƙasar nan, baya ga dubban jami’an tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!