Labarai
Buhari zai ciyo bashi wajen kammala aikin shimfida batutun mai
Gwamnatin tarayya ta ce za ta ciyo bashin sama da dala biliyan biyu daga kasar China domin kammala aikin shimfida bututun mai na Ajakuta da Kaduna da kuma Kano kafin shekarar 2023.
Ministar kudi kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmad ce ta bayyana hakan yayin ziyarar duba aikin shimfida bututun man.
Ta ce, duk da matsin tattalin arzikin da Najeriya ke fuskanta a yanzu, gwamnatin tarayya za ta yi kokarin ganin an kammala aikin kafin shekarar 2023 wanda a yanzu aikin yake tafiyar wahainiya.
Hajiya Zainab ta kuma ce, kammala aikin wani mataki ne da zai samarwa yan Najeriya ayyukan yi musamman matasa da kuma farfado da tattalin arzikin kasar.
Ministar ta kuma bukaci kamfanin da aka bai wa kwangilar aikin mai suna Oilserv da ya tabbatar ya gudanar da ayyukansa yadda aka bukata ba tare da kawo tsaiko ba, wanda hakan ne ya sanya gwamnatin ciyo bashi daga kasar ta China don kammala aikin.
You must be logged in to post a comment Login