Labarai
Buhari zai raba kayan abinci ga gidaje fiye da dubu 20 a jihar Borno
Gwamnatin tarayya ta raba tallafin kayan abinci ga gidaje dubu ashirin da da shida da sittin da bakwai a Jihar Borno, sakamakon iftila’in hare-haren kungiyar Boko Haram da kuma ambaliyar ruwa.
Ministan ma’aikatar jin kai da takaita iftila’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Farouk ce ta sanar da hakan lokacin da take yi wa mataimakin gwamnan Jihar Borno Alhaji Umar Kadafur karin haske yau a birnin Maiduguri.
Sadiya Farouk ta ce ta je Maiduguri ne a madadin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo domin tattauna irin gudunmawar da al’ummar jihar Borno ke bukata a cikin wannan yanayi.
Kayayyakin abincin da ministar ta bayar sun hdar da buhun shinkafa mai nauyin kilo 12.5 guda 26,067, buhun wake mai nauyin kilo 25 guda 26,067, sai buhunan masara da da gero masu nauyin kilo 12.5 guda 26,067.
Sauran su ne buhun gishiri mai nauyin kilo 20 guda 1,304, sai man girki da sinadarin dandanon girki da tumatur.
A na sa jawabin mataimakin gwamnan Jihar ta Borno Alhaji Umar Kadafur ya godewa gwamnatin tarayya bisa tallafin tare da alkawarin ci gaba da aiki da dukkan hukumomin tsaron kasar nan wajen ganin an kawo karshen matsalolin tsaron da yankin ke fuskanta.
You must be logged in to post a comment Login