Labarai
Buhari zai raba mitar wutar lantarki miliyan 36 cikin watanni uku masu zuwa
Hukumar kula da bangaren samar da wutar lantarki ta kasa, ta ce, nan da watanni uku masu zuwa, za a sanyawa gidaje akalla miliyan talatin da shida mitar wutar lantarki a fadin kasar nan baki daya.
A cewar hukumar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya ba da wannan umarni.
Karamin ministan samar da wutar lantarki, Goddu Jedy-Agba ne ya bayyana haka a jiya juma’a, jim kadan bayan duba aiki a wani kamfanin gwajin na’urar mitar lantarki a jihar Enugu.
Ya ce nan da makwanni shida masu zuwa ne ake sa ran za a kaddamar da kamfanin gwajin mitar.
A cewar sa manufar kafa kamfanin gwajin mitar ita ce, tabbatar da cewa duk mitoci da za a shigo da su kasar nan sun cika duk ka’idoji da ake bukata.
You must be logged in to post a comment Login