Labarai
Buhari zai raba motocin safa don rage radadin karin farashin mai
Gwamnatin tarayya ta ce ta kammala shirye-shirye domin rarraba wasu motocin safa-safa guda dubu biyu a sassa daban-daban na kasar nan, don ragewa al’umma illar da karin farashin litar mai zai yi musu.
A cewar gwamnatin motocin za su mai da hankali ne wajen jigila a yankunan karkara.
Ministan ayyuka na musamman Dr. George Akume ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja.
Ya ce, wannan wani yunkuri ne da ma’aikatar ayyuka na musamman da ma’aikatar aikin gona da bunkasa karkara da kuma wasu hukumomin gwamnati ke yi da nufin ragewa jama’a radadin da karin farashin mai zai yi musu.
Ministan ya ce, gwamnati za ta raba motocin ne ga kungiyoyi maimakon ba da shi ga daidaikun mutane wanda zai janyo tsaiko wajen gudanar da shirin cikin nasara.
You must be logged in to post a comment Login