Connect with us

Labarai

Salon mulkin Buhari ya raba kan Najeriya – Obasanjo

Published

on

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce, Najeriya ta gaza kuma tana daf da zama kasa da ke neman rugujewa.

Olusegun Obasanjo ya ce Najeriya ta rabu gida-gida sakamakon salon mulki na shugaba Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke gabatar wata makala a wajen wani taron tuntuba da aka gudanar a Abuja.

Obasanjo ya ce rarrabuwar kawuna da kin jinin juna sai kara yawa yake a kasar nan sakamakon yadda gwamnati ke jagorantar kasar.

Taron dai an gudanar da shine a ranakun tara zuwa goma ga wannan wata a birnin tarayya Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,772 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!