Labarai
Bashin da ake bin Najeriya ya ninka kasafin kudin badi-Akibu Hamisu
Babban daraktan cibiyar bibiya da tsage gaskiya da yaki da cinhanci da rashawa ta Africa Kwamared Akibu Hamisu ya ce bashin da ake bin Najeriya a yanzu ya ninka kasafin kudin da kasar nan tayi a kasafi n kudin shekarar 2019 domin ya tasamman sama da tiriliyan Ashirin da bakwai.
Kwamared Akibu Hamisu ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Muleka mu gano na musamman na Gidan Redio Freedom daya mayar da hankali kan basukan da ake bin Najeriya a yanzu.
Akibu Hamisu ya kara cewa da bashin da kasar nan ke ciyowa ana amfani da su ta hanyar da da suka dace kuma mutane suna amfana dashi al’ummar kasa baza su damu ba.
Shugaban Cibiyar Akibu Hamisu ya kara da cewa ciyo bashi da Najeriya ke yi babu wani abu da zai jawowa kasar nan face koma baya musamman yadda ake ware makudan kudade domin biyan bashin da aka ciyo daga wasu kasashe.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa daya bibiyi yadda shirin ya gudana ya ruwaito shugaban cibiyar Akibu Salihu na cewa ya zama wajibi kasar nan ta rage ciyo basuka daga kasashe kuma Najeriya ta cigaba da biyan basukan da ake binta wajen bazama don neman yafiya akan basukan da ake bin ta kasancewar ta hakane za’a sami mafita.