Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Buhari, Zulum, Kwankwaso, El-Rufai- Wa Nigeria ta fi bukata a cikinsu?

Published

on

Daga Abdullahi Isah.

Ko da ya ke idan aka bi tsarin da kasar nan ke bi ta karba-karba bako shakka yankin Arewa ba zai yi mafarkin sake komawa mulki a shekarar dubu biyu da ashirin da uku ba (2023) saboda kokari da al’ummar daya bangaren kasar nan za su yi wajen ganin mulki ya koma garesu.

Duk da cewa sanannen abune wannan batu na karba karba tsakanin kudu da Arewa ba tsari bane da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar nan hasalima wata jamiyya ce ta amince da hakan a matsayin maslaha.

Sai dai Kuma bako shakka yanzu lamarin ya wuce yadda kowa ke tsammani don a duk lokaci da wani bangare ya gama zangon Shekaru 8 sannan ya nemi ya zarce to akan fuskanci matsaloli da dama.

Amma tunda batu ne na siyasa ba za a ce sam har abada hakan bazai taba canjawa ba saboda a siyasa komai na iya faruwa musamman ganin cewa wannan bangare bai samu goyon bayan kundin tsarin mulkin kasar nan ba.

To koma menene Allah shi ne masanin kome zai faru Shekaru hudu masu zuwa, amma alal misali idan ya kasance wannan tsarin ya wargaje sannan ‘yan siyasa su ka bai wa kowane bangare na kasar nan ya nemi mulkin kasar nan, akwai mutane uku wadanda ake kallon su cikin masu karancin Shekaru da Kuma ake musu kallon hazikai wadanda matukar aka basu dama wajen mulkin kasar nan, za su yi abin azo a gani.

Shugaba Buhari dai sanan nen abune daga shekarar dubu biyu da ashirin da uku zai bar mulkin kasar nan gudunmawa da ya bayar kuwa watakila sai karshen mulkin sa za a tantance hakan.

Saboda haka za mu fi ma i da hankali kan mutane uku wato gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno da takwaransa na jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da Kuma tsohon gwamnan jihar Kano Engineer Rabi’u Musa Kwankwaso, wadanda sune ‘yan siyasa daga Arewacin kasar nan da a yanzu ake ganin tauraruwar na haskawa.

Farawa da gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda Injiniya ne kan harkokin noma a jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno kafin shiga harkokin siyasa. Babagana Umara Zulum, tun bayan rantsar da shi a matsayin gwamna na jihar Borno tauraruwar sa ke ta haskawa ba wai a jihar sa ta Borno ba kawai ko Arewacin Najeriya.

 

Yanzu lamarin ya kai al’ummar kasar nan daga kowane bangare yaba irin salon mulkin sa suke musamman wajen nuna damuwa da halin da talakawan jihar Borno ke ciki.

Gwamna Babagana Umara Zulum a yanzu ya zama dan mowa tsakanin alummar kasar nan cikin kankanin lokaci, wanda yanzu hankula sun karkata gareshi kowa sai fatan alheri ya ke masa tare da kiraye-kirayen neman da a tsayar da shi takara idan shugaba Buhari ya kammala wa’adin mulkin sa.

Malam Nasir Ahmed El-Rufai shine gwamna mai ci na jihar Kaduna a yanzu, ba ko shakka wannan bawan Allah tun bayan shigar sa fagen siyasa a lokacin mulkin Obasanjo ya zama abin nan da masu iya magana ke cewa Kadangaren bakin Tulu a kasheka a fasa Tukunya a kyaleka ka yi barna.

Abinda nake anan dai shi mutum da ya ke da halin ya fyadi yaro ya fyadi babba aduk lokacin da ya samu dama ba ya daga kafa ga kowa ciki kuwa har da jami’an gwamnati da ya ke musu aiki.

Malam Nasir El-Rufai ba mutum bane matsoraci Kuma ba ya shakkar daukar mataki komai dacin sa kuma ko da kuwa zai bakanta ran wasu ciki kuwa har da na gaba da shi, matukar ya yi imanin cewa abinda ya ke son yin nan daidai ne.

Kadan daga cikin tsauraran da gwamna Nasir Ahmed El-Rufai ya dauka lokacin yana ministan birnin tarayya ds Kuma yanzu da bya zama gwamnan jihar Kaduna sun hada da:

Rushe gidaje a birnin tarayya wadanda aka ginasu ba bida ka’ida ba wanda mataki ne da yanyo mishi makiya da masoya. Haka zalika El-Rufai ya dauki wani mataki wajen korar malamai da basa da kwarewar aiki a jihar Kaduna wanda shima mataki ne da ya janyo mishi makiya da Kuma masoya.

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano ne har sau biyu Kuma tsohon Sanata Wanda Kuma ya taba zama ministan tsaro. Rabiu Musa Kwankwaso ya samu dumbin magoya baya sakamakon rawwar da ya taka wajen bijiro da ayyukan raya kasa a jihar Kano lokacin yana gwamna.

Dr Rabiu Kwankwaso daya daga cikin bangarori da magoya bayansa ke tutiya da shi shine gudunmawar sa bangaren ilimi wajen kirikiro da jihohi guda biyu mallakin jihar da wasu manyan makarantun gaba da sakandire da dama da Kuma gudanar da ayyukan raya kasa kamar du gada da tituna da sauransu.

Haka zalika bayan barinsa mulki ya ci gaba da gudanar da wasu ayyukan kamar daukar nauyin dalibai zuwa ketere don karatu da dai sauran su.

Wadannan mutane uku bako shakka sune tauraruwar su ke haskawa cikin Yan siyasa da suka fito daga yankin Arewa wadanda jama’a ke ta fatan ganin daya daga cikinsu ya damu damar mulkar kasar nan a nan gaba.

Ni dai gareni kowa daga cikinsu ya cancanta, saboda haka shawara ya rage ga jama’a su ga wa tafi cancanta cikin mutane ukun don jagorantar kasar nan a nan gaba.

Rubutu daga Abdullahi Isah

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!