Labarai
BUK ta haramta yin amfani da sunanta ko tambarinta a kafafen sada zumunta

Jami’ar Bayero da ke Kano, ta haramta yin amfani da sunanta ko tambarinta a kafafen sada zumunta ba tare da sahalewa daga gare ta ba, domin kare ƙima da sahihancin bayanan jami’ar.
Wannan na cikin sanarwar da Daraktan Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Malam Lamara Garba, ya fitar a madadin Rijistarar makarantar.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’ar ta lura da yawaitar amfani da sunanta da tambarinta ba bisa ƙa’ida ba daga mutane ko ƙungiyoyi a kafafen sada zumunta, abin da ke iya sanya rudani ga ɗalibai, masu neman gurbin karatu da sauran al’umma.
Sanarwar ta ƙara da cewa an umarci duk masu amfani da sunan jami’ar ko tambarinta ba tare da izini ba da su goge su nan take, tare da gargadin cewa duk wanda ya saɓa wa wannan umarni zai fuskanci matakin da za su ɗauka na gaba.
You must be logged in to post a comment Login