Labarai
BUK ta kori dalibai 63 saboda satar jarrabawa
BUK ta kori dalibai 63 saboda satar jarrabawa
Jami’ar Bayero dake nan Kano ta kori dalibai 63 sakamakon kama su da laifuka daban-daban na magudin jarrabawa.
Daraktar sashen kula da jarrabawa da daukar dalibai da kuma adana bayanai ta jami’ar Hajiya Amina Abdullahi ce ta sanar da hakan a yau, tana mai cewar an kuma dakatar da wasu karin dalibai guda 13 har na tsawon shekara guda sakamakon samun su da aikata laifin,satar jarrabawa.
Hajiya Amina Abdullahi ta shaida cewa matakin ya biyo bayan amincewar da kwamitin kula da jarrabawa na majalisar gudanarwar Jami’ar yayi, bayan kammala taron sa karo na 374 a ranar 28 ga watan Agustan da ya gabata.
Ta kara da cewa dalibai goma daga cikin wadanda aka sallama sun fito ne daga sashin nazari kan digiri na biyu wato Postgraduate Studies sai kuma bakwai daga sashin ci gaban karatu.
Sauran su ne dalibai bakwai daga sashin kimiyyar lafiya da bakwai daga sashin nazari kan ilimin kimiyyar kwamfiyuta, sai kuma dalibai shida daga tsangayar nazarin ilimi da na nazarin harkokin Injiniya da kuma sha’anin gudanarwar kimiyya da fasaha.