Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

BUK zata fara gwajin masu dauke da cutar Corona

Published

on

Cibiyar gwaje-gwajen cututtuka masu yaduwa ta Jami’ar Bayero dake nan Kano ta ce a gobe ne zata fara gudanar da gwajin mutanan da ake zargin suna dauke da cutar Corona.

Shugaban cibiyar Farfesa Isah Sadik Abubakar ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da Freedom Radiyo game da yadda aikin cibiyar ke gudana.

Farfesa Isah Sadik Abubakar ya kuma ce cibiyar Zata yi hadin gwiwa da cibiyar dakile cutuka ta kasa NCDC, inda zata rika gudanar da gwajin akalla mutane dari da tamanin a rana daya.

Farfesa Isah Sadik Abubakar ya kuma ce jami’ar ta Bayero karkashin shugaban ta Farfesa Muhammad Yahuza Bello ta fitar da sama da naira miliyon Hamsin don gudanar da aikin gwaje-gwajen cutar ta Covid-19 a cibiyar.

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni dake nan Kano dama kasa baki daya dasu tallafawa cibiyar da abubuwan da suka kamata don ganin cibiyar ta ci gaba da gudanar da ayyukan ta yadda ya kamata.

Haka zalika Freedom Radiyo tayi kokarin jin ta bakin sashen gudanar da gwajin cutar ta Corona dake Asibitin Aminu Kano game da cigaba da aikin gwajin, sai dai hakan bai yiwuba kamar sakamakon rashin samun wanda zai Magana aka yi.

Sai dai Freedom Radio ta tuntubi wani likita dake aiki a sashen da ake gudanar da gwajin a Asibitin, inda ya shaida mana cewa duk waddanda ke da alhakin yin Magana a kai suna aikin gudanar da gwaje-gwaje a dakin a lokacin a don haka ba za su iya tattaunawa da mu ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!