Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Burinmu shi ne a riƙa Noma Kadada Miliyan daya nan da 2028- TOURBA

Published

on

Yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin ɗumamar yanayi a duniya, kamfanin bunƙasa harkokin Noma na Tourba, ya gudanar da taron masu ruwa da tsaki karon farko a jihar Kano domin tallafa wa manoma ta yadda za su amfana da dabarun bunƙasa Noma da kuma samun amfanin goma fiye da yadda suke samu a baya.

Da ya ke jawabi ga manema labarai yayin Ƙaddamar da shirin, a yau Litinin, shugaban gudanarwar harkokin kamfanin Mista Bouris Nague, ya bayyana cewa, wannan ne karo farko da suka kaddamar da aikinsu a jihar Kano don haka suna fatan manoma da dama za su amfana da irin tallafin da suke bayarwa don bunkasa harkokin noma.

“Mun samu nasarori da dama a Najeriya bayan da muka kaddamar da wannan aiki a jihohin Nasarawa da Niger, zuwa yanzu fiye da manoma 500,000 ne suka rungumi wannan tsari, kuma muna fatan mu shi ne a riƙa Noma fiye da Kadada miliyan 1 daga yanzu zuwa shekarar 2028″ in ji shi.

Haka kuma ya ƙara da cewa, Don haka muna kira masu ruwa da tsaki a wannan fanni da su bamu haɗin kai don samun nasara a wannan aiki kamar yadda muka samu nasarori a kasashen da muka gudanar da wanan aiki”.

Shi ma a nasa bangaren, babban malamin Gona na Tourba a nan Najeriya Malam Yusuf Ali Bello, cewa ya yi, suna so manoma su rungumi tsarin ne wanda ba sabo ba ne, hanya ce da aka jima ana amfani da ita wadda ta hada da yin amfani da ƙananan kayan aikin gona sakamakon yadda aka gano yin aiki da manyan kaya kamar Tantan ya na rage karfin ƙasa wanda hakan ke hana amfani yin kyau.

“Idan Manoma suka rungumi wannan tsari za su amfana da abubuwa guda uku a takaice, na farko shi ne za su samu amfanin gona fiye da wanda suka saba samu a baya, sai kuma kara ingancin Kasar Noma da kuma samar wa manoma karin kudaden shiga”.

“idan manoma suka karbi wannan shiri namu, za su amfana matuka, don haka muka tattaro masu ruwa da tsaki don su isar da sako ga manoma ta yadda abinda muke son cimma zai isa ga kowa, inji Malam Yusuf Ali Bello.

Da ya ke gabatar da jawabi a taron, kwamishinan ma’aikatar Muhalli da magance ɗumamar yanayi na Kano Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana jin dadi bisa shirya taron tare da cewa gwamnati za ta bai wa Tourba dukkan haɗin kan da ya dace wajen ganin sun cimma burinsu.

“A matsayin mu na gwamnati, za mu bada dukkan goyon baya wajen ganin wannan ƙuduri ya samu nasa matuka ta yadda manomanmu za su samu ƙaruwar arziki kamar yadda muke fata, inji Kwamishinan.

Haka kuma ya ce, Muna kira ga manoma da sauran masu ruwa da tsaki a wannan fanni, da su tabbatar sun rungumi wannan tsari dari bisa dari domin ci gaban jihar Kano da Najeriya har ma da duniya baki daya.

Taron wanda aka gudanar a Kano, ya samu halartar masu ruwa da tsaki da suka hadar da jami’an gwamnati da shugabannin Kungiyoyin Manoma da ƴan kasuwa da masu rike da sarautun gargajiya da sauransu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!